1 Timothy 2

1Don haka da farko dai, Ina roko a yi roke-roke da addu‘o’i, da yin roko domin jama, a dukka, da ba da godiya, a yi haka domin dukkan mutane, 2domin sarakuna da dukkan masu mulki, domin mu yi zaman salama da rayuwa a natse cikin Allahntaka da daraja. 3Wannan yana da kyau da karbuwa a gaban Allah mai cetonmu. 4Yana so dukkan mutane su sami ceto, su kai ga sanin gaskiya.

5Domin Allah daya ne, Matsakanci kuma daya ne, tsakanin Allah da mutum, wannan mutum Almasihu Yesu ne. 6Ya bada kansa fansa domin kowa, domin shaida a daidaitaccen lokaci. 7Sabo da wannan dalilin, aka sa ni kaina, na zama mai shelar bishara da manzo. Gaskiya nake fada. Ba karya nake yi ba. Ni mai koyarwa ne na al’ummai cikin gaskiya da kuma imani.

8Saboda haka, ina so maza da ke a kowanne wuri suyi addu’a, kuma suna daga hannuwa masu tsarki a sama ba tare da fushi da gardama ba. 9Kazalika, ina so mata su sa kayan da ya cancanta, da adon da ya dace da kamun kai. Kada su zama masu kitson gashi da zinariya da azurfa da tufafi masu tsada. 10Ina so su sa tufafin da ya cancanci matan da ke rayuwar Allahntaka ta wurin kyawawan ayyuka.

11Mace ta koya cikin natsuwa da saukin kai a cikin komai. 12Ban ba da izini mace ta koyar ko ta nuna iko a kan namiji ba, amma ta zauna da natsuwa.

13Adamu ne aka fara halitta, kafin Hauwa’u. 14Ba Adamu ne aka yaudara ba, amma macen ce aka yaudara cikin laifi. Duk da haka, zata sami ceto ta wurin haifuwar ‘ya’ya, idan suka ci gaba cikin bangaskiya, da kauna da tsarki da sahihiyar zuciya.

15

Copyright information for HauULB